An amince a tsige shugabar Brazil

Shugabar kasar Brazil Dilma Roussef za ta fuskanci tuhuma da kuma dakatarwa daga aiki bayan 'yan majalisar dattawan kasar sun amince a tsige ta.

Ana zargin ta ne da boye gagarumin gibi a asusun kasar gabanin sake zaben ta a shugaban in kasar a shekarar 2014, sai dai ta sha musanta zargin.

'Yan majalisa 55 sun amince a dakatar da ita daga mulki, yayin da 22 suka ki amincewa bayan sun kwashe awowi 20 suna kada kuri'a.

Mataimakinta, Michel Temer, zai maye gurbin ta a yayin da Za a yi mata shari'a.

Da ma dai ta zargi shi da hannu a yunkurin yi mata juyin mulki.