Za a fallasa masu boye kaddarori a Biritaniya

Hakkin mallakar hoto Getty

Mista Cameron ya yi wannan sanarwar ne a wani mataki na magance matsalar cin hanci da rashawa.

Mista Cameron ya ce daga yanzu kamfanoni za su rika bayyana kaddarorinsu a wata sabuwar rijista.

Ya bayyana haka ne a yayin da Biritaniya ke yunkurin jagorantar wani shiri na dirar wa masu hannu dumu-dumu a cin hanci da rashawa a fadin duniya.

Ana zargi manyan kamfanoni da masu kudin kasashen duniya, ciki har da Najeriya, da sace kudade suna sayen gidaje da sauran manyan kaddarori a Biritaniya.

A ranar Laraba ne dai shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci Firai Minista Cameron ya dawowa da Najeriya kaddarorin da wasu manyan jami'an gwamnatocin da suka gabata suka saya a Biritaniya, bayan Mista Cameron ya ce Najeriya da Afghanistan su ne kan gaba wajen cin hanci a duniya.