Musulmi: Trump ya yi amai ya lashe

Hakkin mallakar hoto Getty

Da alamu dai dan takarar ya yi amai ya lashe kan aniyarsa ta hana Musulmai shiga kasar ta Amurka, idan ya ci zaben da za a yi a watan Nuwamba mai zuwa.

A lokacin da ya ke mayar da martani a kan jawabin da sabon magajin garin London, Sadiq Khan ya yi, mista Trump ya shaida wa gidan radiyon Fox da ke Amurka cewa dama ai "Shawara ce".

Mista khan dai ya bayyana damuwar cewa ba zai iya zuwa Amurka ba a lokacin mulkin Trump saboda shi Musulmi ne.

Trump dai ya ce zai daga kafa ga sabon magajin garin na London.

Amma Mista Khan bai amince da hakan ba, inda ya ce Donald ya jahilci Musulunci kuma matakin hana musulmai shiga Amurkan zai iya sanya Amurka da ma Burtaniya cikin hatsari.