Hajj: An kasa daidaitawa tsakanin Saudi da Iran

Hakkin mallakar hoto Getty

Saudi Arabia ta musanta cewa, ita ce take da alhakin kasa samun daidaito tsakaninta da Iran dangane da baiwa 'yan Iran damar yin aikin Hajjin bana.

Iran ta zargi Saudiyya da ƙin bada haɗin kai kwata-kwata yayin tattaunawa akan batun.

Amma Saudiyya ta ce, Iran ce ta ƙi bada haɗin kai, dan haka aka gaza cimma yarjejeniya.

Dangantaka tsakanin ƙasashen biyu masu faɗa-a-ji ta taɓarɓare.

Ƙasashen biyu dai sun yi cece-kuce yayin aikin Hajjin bara inda ɗaruruwan mahajjatan Iran suka mutu yayin tumutsutsun da aka yi a Muna