Kenya ta keta dokokin WADA

Wani kwamitin hukumar yaki da shan kwayoyin kara kuzari ta duniya ya bayar da shawarar cewa a bayyana Kenya a matsayin wadda ta saba dokokin yaki da shan miyagun kwayoyi.

Wannan dai wani mataki ne da ka iya hana 'yan wasannin guje-guje da tsalle tsalle na Kenya zuwa gasar wasannin Olympics da za'a yi a Rio.

Wani wakilin BBC kan harkokin wasanni ya ce ana sa ran hukumar ta amince da shawarar a wajen taron da za su yi a Canada.

Zai kuma rage ga kwamitin gasar wasannin Olympics na yanke shawarar hana Kenyan shiga gasar.