An kori wata ma'aikaciya saboda rashin sa takalmi mai tsini

An kori wata ma'aikaciya mai karɓar baƙi a wani kamfani a London saboda ta ƙi saka takalmi mai tsini.

Nicola Thorp mai shekara 27, 'yar garin Hackney da ke Birtaniya, wadda take aiki na wucin gadi a kamfanin harkokin kuɗi na PWC, an shaida mata cewar sai ta dinga saka takalmin da tsayinsa ya kai inci biyu zuwa huɗu.

Bayan ta ƙi amincewa kuma ta yi ƙorafi a kan cewa ba a ce wa abokan aikinta maza su yi hakan ba, sai aka kore ta ba tare da an biya ta kuɗinta ba.

Kamfanin Portico ya ce, Ms Thorp ta riga ta saka hannu a kan dokokin tsarin shigar da kamfanin ya ke so a dinga yi amma kuma zai sake duba yiwuwar sauya su.

PwC ya ce yanayin shiga ba tsarinsa ba ne.

Ms Thorp ta za ta sha wahala wajen zuwa aiki idan ta saka takalami mai tsayi har tsawon sa'oin da zata shafe tana aiki, kuma ta tambaya a barta ta saka takalmi mara tsayin da ta saka a lokacin da ta fara aikin.

Amma sai aka gaya mata cewa ta sayi takalmi mai tsayi a ranar da ta fara aiki a watan Disamba.

Ta ce, "Sai na ce idan har za su iya bani dalilin da saka takalmi mara tsayi zai hana yin aiki a yau, to zan yi, amma sai suka kasa, kamar yadda Ms Thorp ta shaidawa gidan rediyon BBC da ke London.

"An bukaci na yi sa'oi 9 ina sanye da takalmi mai tsayi kuma na raka baƙi zuwa ɗakunan da ake ganawa da su. Na ce ba zan iya yin haka ina sanye da takalmi mai tsayi ba.

Ms Thorp ta ce ta yi tambayar ko za a buƙaci namiji ya kwashe wannan sa'oin yana aiki sanye da takalmi mai tsayi, sai aka dinga yi mata dariya.

Bayan an yi haka ne sai ta shaida wa ƙawayenta abinda ya faru kuma bayan sun wallafa a shafin sada zumunta da muhawara na Facebook sai ta gano cewa wasu matan ma suna samun kansu a cikin irin halin da ta tsinci kanta a ciki.

A cewar Thorn, "A da na ji tsoron na fito na yi magana a kan lamarin, amma kuma sai na gano cewar dole ne na yi magana saboda al'amarin babba ne."

Mutane sama da dubu 10,000 sun saka hannu a kan bukatar Thorn, na a sauya dokar ta yadda ba za a tirsasawa mata saka takalmi mai tsayi ba a wajen aikinsu. Saboda haka yanzu, dole gwamnati ta mayar da martani a kan lamarin.

Hakan ya dace a doka?

A yadda dokar take a yanzu, za a iya korar ma'aikata daga aiki idan har basu bi ƙa'idar yanayin saka kaya ba in har an basu isasshen lokacin da za su sayi takalmin da ya dace da kuma kayan sakawa.

Za su iya wanzar da tsarin saka kaya na mata da maza, idan har dukkansu za su daidaita a "wajen fitowa fes-fes".

Ms Thorp ta ce, "Bani da wani ja da kamfanin saboda sun yi amfani ne da damar da suke da ita a matsayinsu na wadanda suke ɗaukar ma'aikata na samar da tsarin saka kaya, kuma wani ɓangare na dokar, shi ne saka takalmi mai tsayi.

Ta ce, "Ina ga ya kamata tsarin saka kaya ya tafi daidai da al'umma kuma a kwanakin nan mata suna iya fitowa fes ba tare da sun saka takalmi mai tsayi ba.

Manajan darakta na kamfanin Portico ya ce, ''Ba sabon abu bane a sashen ma'aikatu a samar da tsarin saka kaya," wanda Thorp ta yarda da shi.

Ya ƙara da cewa, irin waɗannan tsare-tsaren na tabbatar da cewa a ko da yaushe ma'aikata na bayyana kansu cikin yanayin shiga mai kyau da kuma gamsar da abokan hulɗarsu.

Duk da haka, ya ce kamfanin ya yi maraba da ra'ayoyin mutane a kan lamarin kuma zai sauya ka'idojin."

Wani mai magana da yawun PwC ya ce kamfanin na tattaunawa da Portico a kan tsare-tsaren.

"PwC ba shi da tsarin saka kaya na mussaman ga ma'aikatansa maza da mata."