Kungiyoyi sun soki karin farashin mai

Kungiyar kwadago ta Nigeria ta ce, ba ta yarda da karin kudin man fetur da gwamnatin ta yi ba.

Karin kudin man dai, ya biyo bayan cire tallafi mai da gwamnatin ta yi.

Kuma za a sayar da lita daya ta man fetur kan Naira 145.

Sakataren yada labarai na kungiyar kwadago ta Najeriya wato NLC, Comrade Nuhu Abbayo Toro ya ce, ba zasu amince ba da karin farashin.

NLC ta ce, zata dauki mataki kan karin kudin man da aka yi nan gaba bayan wani taro da za ta gudanar.