Ana taron koli a kan tsaro a Nigeria

Image caption Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai gana da takwaransa na Faransa Francois Hollande

A Najeriya, a yau ne kasashen da ke yankin tabkin Chadi ke fara wani taron koli a kan harkokin tsaro, inda ake sa-ran duba irin nasarorin da aka samu a kokarin da ake yi na murkushe kungiyar boko Haram da kuma yadda za'a taimaka wa wadanda rikicin ya shafa.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ne zai karbi bakuncin taron wanda zai samu halartar shugaban kasar Faransa Francois Hollande, da shugabannin kasashen Kamaru da Nijar da Chadi da kuma Jamhuriyar Benin.

Kazalika wakilai daga kasashen Amurka da Ingila da Equitorial Guinea da kungiyoyin tarayyar turai da na Ecowas da kuma hukuma mai kula da gabar tekun Guinea za su halarci wannan taro.

Taron dai zai fi mayar da hankali ne a kan yaki da kungiyar Boko Haram da ake yi a yanzu, sannan taron zai duba yadda za a magance irin matsalolin da rikicin Boko Haram ya jefa mutane a ciki.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake gudanar da irin wannan taro,inda aka gudanar da na farko a shekarar 2014 a kasar Faransa.