Brazil: Temer ya nemi goyon baya

Hakkin mallakar hoto getty

Shugaban rukon kwaryar na Brazil, Michel Temer ya sanar da cewa, wasannin Olympics na Rio a watan Agusta mai zuwa za su bai wa kasar Brazil wata dama ta musamman don nuna wa duniya gaskiyar lamarin tattalin arzikinta da kuma siyasarta.

Shugaban rukon kwaryar, ya yi kira ga 'yan kasar ta Brazil da su kasance tsintsiya madaurinki daya, wajen yin aiki tare da gwamnatinsa domin ciyar da kasar gaba da kuma sake farfado da kimarta a idon duniya, bayan cece-kucen siyasa da ta fuskanta.

A cikin jawabinsa na farko tun bayan da ya maye gurbin Shugaba Dilma Rousseff, da aka dakatar don fuskantar shari'ar tsigewa, mista Temer ya shaidawa 'yan kasar ta Brazil cewa, ya kamata su amince da irin cigaban da dumokaradiyar kasar take da shi.

A nata bangaren kuma, Dilma Roussef, ta ce za ta yi amfani da dukkan hanyoyin shari'a da suka dace, wajen fafutuka da tsigewar da ake son yi mata.