'Yadda zamu mayar wa Nigeria kudade'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Firaiministan Burtaniya, David Cameron da John Kerry da Buhari

Fira Ministan Burtaniya, David Cameron ya sanar da yadda za a taimaka wajen maido wa kasashe da kuɗaɗen da aka sace musu.

Cameron dai fitar da sanarwar ne a ƙarshen babban taron da aka gudanar a birnin Landan, a kan cin hanci da rashawa.

A karkashin tsarin, gwamnatoci da hukumomin tsaro za su gabatar da wani taro domin tattaunawa kan yadda za a mayarwa Najeriya da Ukraine da Srilanka da kuma Tunisia, kudaden nasu.

Za a gabatar da taron ne a Amurka a 2017 bisa hadin gwiwar Burtaniya da Majalisar Dinkin Duniya da Bankin Duniya.

Ana dai zargin Burtaniya da matattarar boye kudaden da ba halattattu ba.