Nigeria: 'Ƙarin kuɗin mai ba zai magani ba'

Image caption Kimanin shekara guda ke nan ana fama da matsalar mai a Najeriya.

Ƙungiyar 'yan kasuwa masu sayar da man fetur masu zaman kan su ta Nigeria IPMAN, ta ce cire tallafin mai ba zai zama hanyar kawo karshen matsalar karanci da tsadar man ba a Najeriya.

Kungiyar ta bakin shugabanta na shiyyar Arewa maso yammaci, Alhaji Lawal Muhammad Danzaki, ta kuma ce 'ya'yanta sun faɗa tsaka mai wuya tun bayan da gwamnatin kasar ta janye tallafin man fetur, wanda ya sa farashin sa kai Naira 145 kowacce lita.

A hirarsa da wakilinmu na Kano, Yusuf Ibrahim Yaksai, Alhaji Danzaki ya ce a sabon tsarin ba a ƙayyade yadda za su sayi man ba daga 'yan kasuwar da ke shigo da shi daga waje ba.

Amma su an ƙayyade musu yadda za su sayar, abinda kuma ya sa suka ce, a yanzu haka matsalar ke neman ƙarewa a kansu.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti