Ƙungiyar ƙwadago na taro a Nigeria

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Zanga-zangar da NLC ta jagoranta a 2012.

Ƙungiyar ƙwadago a Najeriya wato NLC, na wani taron gaggawa a Abuja, babban birnin ƙasar, domin ɗaukar mataki kan janye tallafin mai da gwamnatin ƙasar ta yi.

A ranar Laraba ne dai ministan man ƙasar, Ibe Kachukwu ya sanar da janye tallafin man, abin da ya sanya aka ƙara ƙudin mai daga Naira 86.50 zuwa 145 a kan kowace lita.

Tuni ƙungiyar ta ƙwadago ta yi watsi da sabon tsari, a inda kuma ta ce za ta kira taro ranar Juma'a domin tattauna irin matakin da za ta dauka.

Ko a 2012 ma, ƙungiyar ta ƙwadago ta jagoranci zanga-zanga mai taken 'Occupy Nigeria' wajen nuna kin amincewa da cire tallafi da gwamnatin Goodluck Jonathan ta yi.

Yanzu haka, ana jiran sakamakon taron ƙungiyar ta NLC.