Niger: Hafsoshin sojin yankin tafkin Chadi za su fara taro

Hakkin mallakar hoto none

A Jamhuriyar Nijar, a yau ne manyan hafsoshin sojin kasashen yankin tabkin Chadi za su fara wani taro na kwana biyu a birnin Diffa.

Kazalika an gayyaci masana a kan harkar tsaro zuwa wajen taron domin nazarin kalubalen da ake fuskanta a yakin da ake yi da ta'addanci a yankin.

Kasashen dai sun hada da Kamaru da Chadi da Najeriya da kuma Nijar da kuma Benin.

Taron dai zai gudana ne a karkashin jagorancin masana da suka kware da kuma hadin gwiwar hukumar koli mai kula da wanzar da zaman lafiya a Nijar.

Wadanda suka shirya taron sun ce wannan taro wata dama ce da za a tattauna a kan matsalar da tsaro ke fuskanta da kuma lalubo hanyoyin magance ta.