Hollande zai je Nigeria kan Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP

A ranar Juma'a ne shugaban Faransa, Francois Hollande zai isa Najeriya domin hallartar taro tsaron Afirka na biyu wanda shugaba Muhammadu Buhari zai karbi bakunci, a babban birnin kasar, Abuja.

Shugabanin kasashen Kamaroo da Nijar da Chadi da kuma Benin suma za su halarci taron.

Ana kuma sa ran Amurka da Birtaniya da Equatorial Guinea da tarayyar Turai da kuma kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen nahiyar Afirka ta yamma wato ECOWAS ko CEDEAO za su samu hallartar taron.

Daya daga cikin batutuwan da za a tattauna a taron shi ne na yadda za a shawo kan kungiyar Boko Haram.

An yi taron koli na farko ne dai a watan Mayun shekarar 2014 a birnin Paris.