Pfizer ya hana amfani da magungunansa wajen yin allurar kisa

Hakkin mallakar hoto AP

Kamfanin hada magunguna na Pfizer da ke Amurka ya dauki matakan hana amfani da magungunansa wajen yin allurar kisa.

Cikin wata sanarwa, kamfanin ya ce yana hada magunguna ne don ceton rayukan marasa lafiya, saboda haka bai amince a yi amfani da su wajen zartar da hukuncin kisa ba.

sama da kamfanoni hada magani su 20 daga Amurka da wasu kasashen Turai suka haramta amfani magungunasu wajen zartar da hukuncin kisa, bisa wasu dalilai na kasuwanci ko sanin-yakamata.

Kamfanin Pfizer ya ce zai ci gaba da sa-ido, tare da takaita sayar da wasu magungunansa guda bakwai, wadanda za a iya amfani da su wajen zartar da hukuncin kisa.

Mafi yawanci dai irin kasashen da suke amfani da irin wadannan allura sukan hada magunguna daban-daban sai su yiwa fursuna allurar da zata sa shi bacci daga nan kuma sai numfashinsa ya fara samun matsala hakan ke janyo zuciya ta buga.