EFCC ta kama Shekarau

Hakkin mallakar hoto Getty

A Najeriya Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar, EFCC ta tsare tsohon ministan ilmi na kasar Malam Ibrahim Shekarau.

A jiya ne dai tsohon gwamnan na jihar Kano ya amsa gayyatar hukumar domin amsa tambayoyi kan zargin ya amfana da wani kaso na kudi, Naira miliyan 950 da aka karkata akalarsu wajen yakin neman zaben tsohon shugaba Goodluck Jonathan karo na biyu.

Sai dai mai magana da yawunsa ya shaidawa BBC cewa, ya musanta zargin amfana daga wani kaso na kudin wadanda aka ce an raba a turakarsa.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ku saurari karin bayani a nan.