Tsawa ta kashe mutane 50 a Bangladesh

Hakkin mallakar hoto Kent Wood SPL

'Yan sanda a Bangladesh sun ce mutane fiye da 50 a fadin kasar sun mutu a cikin kwanaki biyu da suka wuce sakamakon tsawa da ta fada musu.

Yawancin wadanda suka rasun manoma ne sun kuma gamu da ajalinsu ne yayin da suke noma a wata gonar shinkafa.

Sauran wadanda lamarin ya ritsa da su sun hada da dalibai a Dhaka babban birnin kasar wadanda su kuma tsawar ta fada musu lokacin da suke buga kwallon kafa.

Sai kuma wani yaron wanda shi kuma ya rasu a lokacin da ya je tsinko mangwaro.

Ana dai yawan samun tsawa da walkiya a Bangladesh amma a bana lamarin ya yi muni matuka.

Kwararru sun yi hasashen cewa tsananin zafi da kuma sare dazuka na iya kasancewa dalilan faruwar hakan.