Shigar 'yan BH Libya barazana ce — Blinken

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mista Blinken ya ce shigar mayakan Boko Haram Libya barazanar tsaro ce

Mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya ce akwai matuƙar damuwa da samun rahoton cewa mayaƙan Boko Haram na shiga Libya, ƙasar da ƙungiyar IS ta fara yin ka-ka-gida a watannin da suka gabata.

Mista Blinken wanda yake halartar taron tsaro na ƙasashen yankin tafkin Chadi da ake yi a Abuja, ya ce alamu sun nuna cewa akwai musayar bayanai tsakanin da taimakekeniya tsakanin Boko Haram da IS ko Da'esh.

Sai dai ya ƙi cewa uffan game da tambayar da aka yi masa, kan ko Amurka za ta sayar wa Najeriya jiragen yaƙi domin yaƙar ƙungiyar Boko Haram.

Sakataren harkokin wajen Biritaniya Phillip Hammond, shima nuna damuwarsa ya yi kan yadda ƙungiyar IS ke sake yaɗuwa a Afrika, da kuma barazanar da har yanzu ƙungiyar Boko Haram ke yi ga zaman lafiya, duk da nasarar da sojoji ke yi wajen ganin sun murƙusheta.

Mista Hammond ya ce Biritaniya tana horar da sojojin Najeriya 1,000 domin cigaba da yaƙar ƙungiyar Boko Haram.

Ya ce, ''Dole mu ƙara jajircewa wajen haɗa kaidomin samun nasara a yaƙin nan, mu kuma samar da muhimman abubuwan da ake buƙata don farfaɗo da yankin da yaƙi ya lalata.''

A yayin da yake nasa jawabin shugaban Faransa François Hollande, ya yabawa mai masauƙin baƙi shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, da kuma ƙoƙarin da shugabannin yankin tafkin Chadi suka yi ta hanyar musayar bayanai, da horas da sojoji da kuma samar da kayan yaƙi.

Taron ya fi mayar da hankali ne a kan yaki da kungiyar Boko Haram da ake yi a yanzu, sannan taron yana duba yadda za a magance irin matsalolin da rikicin Boko Haram ya jefa mutane a ciki.

Wannan dai shi ne karo na biyu da ake gudanar da irin wannan taro, inda aka gudanar da na farko a shekarar 2014 a kasar Faransa.