Babban oditan FIFA ya yi murabus

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shugaban binciken kudi da tabbatar da bin ka'ida na hukumar FIFA ya yi murabus a wani mataki na adawa garanbawul a hukumar kwallon kafar ta duniya.

Dominique Scala ya fusata da matakin baiwa sabuwar majalisar FIFA ikon nadawa da kuma korar mambobin kwamitoci masu cin gashin kan su da ke sa ido kan ayyukan hukumar wadanda suka hada da kwamitocin binciken kudi da da'a da kuma harkokin kudade.

A cikin wata sanarwa Mr Scala yace matakin zai hana wa kwamitocin yanci wajen gudanar da bincike.

Majalisar ita ce ta maye gurbin kwamitin zartarwa FIFA bayan badagakalar cin hanci a hukumar.