Kai tsaye: Taro kan tsaro a Nigeria

Latsa nan domin sabunta shafin

Barkanku da ziyartar shafin BBC Hausa domin samun bayanai kai tsaye a kan taron tsaro da ake yi a Najeriya.

Hakkin mallakar hoto State House

3:48 A wajen taron da yanzu haka yake gudana a otal din Transcorp da ke tarayyar Najeriya Abuja, shugaban kasar Muhammadu Buhari na jawabi kamar haka:

Ya ce, ''Idan na sanya mutane aiki kuma na gaya musu abin da nake so a cimma, to na kan barsu su yi aikinsu.''

Shugaba Buhari ya ce ''Zan tabbatar muku da cewa bana yin katsalandan kan harkokin hukumomin tsaro.''

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin kasashen yankin tafkin Chadi sun yi nasarar rage karfin kungiyar Boko Haram

3:44 *Haka kuma an yi nasarar Shigar da jamhuriyar Benin cikin kungiyar domin bata damar taimakawa makwabtanta.

3:38 Nasarorin da aka samu cikin shekara daya da fara taron tsaro kan kasashen yankin tafkin Chadi:

*Za a sake karfafa rundunar hadin gwiwa ta yankin tafkin Chadi, da dakaru 8,500 daga kassahen Kamaru, da Najeriya, da Benin, wadda za a yi wa shalkwata a Ndjamena babban birnin Chadi.

*An kuma samu nasarar samar da cibiyar hadin kai ta yankin tafkin Chadi a birnin Yaounce na Kamaru, wadda ta samu goyon bayan hukumar kasashen gabar tekun Guinea da ake musayar bayanan tsaro na mambobin kasashen.

3:12 *Za kuma a duba yadda za a yi kokarin nemo dangin kimanin yara 6,000 da suka rasa iyayensu a wannan rikici, wadanda yanzu haka suke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira daban-daban.

Hakkin mallakar hoto AFP

3:11 *Za a karfafa hadin kai tsakanin kasashen yankin domin samar da bayanan sirri a tsakaninsu da kuma abokan huldarsu.

*Za a kara mayar da hankali kan cigaba da neman 'yan matan makarantar Chibok.

3:04 Daga cikin batutuwan da taron zai duba sun hada da:

*Kasashen yankin tafkin Chadi za su bayar da rahoton nasarorin da suka samu da kuma kalubalen da suke fuskanta a yakin da suke da Boko Haram.

*Za su samar da wani shiri na farfado da yankunan da rikicin Boko Haram ya fi yi wa illa, tare da inganta ababen more rayuwa. Gyare-gyaren za su fi mayar da hankali kan cibiyoyin lafiya da makarantu da hanyoyi da kuma samar ruwan sha.

2:57 Tun da misalin karfe 2:30 agogon Najeriya ne shugabannin kassahen da su ke halartar taron suka fara tattaunawa kan batutuwa daban-daban.

2:39 Mr Hammmond ya kara da nuna damuwa kan alakar da ke tsakanin kungiyar Boko Haram da IS ko Da'esh, amma ya ce duk da haka kasashe irin Birtaniya da Amurka na kokarin taimakawa kasashen da ayyukan 'yan ta'adda ya addaba.

2:06 Mista Hammond ya kara da cewa, wannan taro zai yi duba kan yadda za a taimakawa wadannan dubun-dubatar mutane da ke cikin halin ni 'yasu.

1:54 Wakilin BBC Abdullahi Kaura ya tambayi sakataren harkokin wajen Biritaniya Phillip Hammond ko ya yarda da batun shugaban Najeriya cewa an yi nasarar fin karfin kungiyar Boko Haram? Sai ya ce masa, ''Kwarai da gaske sojojin kasar sun yi kokari wajen yaki da kungiyar har ma sun rage mata karfi. Sai dai har yanzu da wata a kasa ta fannin halin ha'u'la'in da mutenen da kungiyar ta tagayyara ke ciki.''

1:38 Shekara biyu kenan da kaddamar da wannan taron, wanda aka yi na farkonsa a birnin Paris na kasar Faransa, wanda aka samar da shi sakamakon kara karfin da kungiyar Boko Haram take yi a wancan lokaci.

1:32 Kwararru kan harkar tsaro na ganin wannan taro da ake yi a Najeriya a wata dama ta yin aiki da Faransa da makwabta wajen kawo karshen kungiyar Boko Haram.

1:30 Kazalika wakilai daga kasashen Amurka da Ingila da Equitorial Guinea da kungiyoyin tarayyar Turai da na Ecowas da kuma hukuma mai kula da gabar tekun Guinea suma suna halartar wannan taro da ake yi a Abuja.

Image caption Boko Haram sun shafe shekaru 6 su na kai hare-hare a kasashen yankin tafkin Chadi.

1:29 A wajen taron shi ma shugaba Francois Hollande na Faransa ya ce, ''Har yanzu kungiyar Boko Haram babbar barazana ce, duk kuwa da irin kokarin da sojoji ke yi na yaki da ita.

Hakkin mallakar hoto Getty

1:24 A yayin da yake jawabi a taron manema labarai, shugaba Buhari ya ce ta'addanci ba ya girmama iyakar kowacce kasa.

1:16 A Najeriya, a yau ne kasashen da ke yankin tabkin Chadi ke fara wani taron koli a kan harkokin tsaro, inda ake sa-ran duba irin nasarorin da aka samu a kokarin da ake yi na murkushe kungiyar boko Haram da kuma yadda za'a taimaka wa wadanda rikicin ya shafa.

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ne zai karbi bakuncin taron wanda zai samu halartar shugaban kasar Faransa Francois Hollande, da shugabannin kasashen Kamaru da Nijar da Chadi da kuma Jamhuriyar Benin.