Damisoshi sun gudu a Netherlands

Damisu Hakkin mallakar hoto
Image caption Damisun sun gudu ne daga wurin da ake tsare da su.

Wasu damisu biyu sun tsere daga gidan ajiyar namun daji a kasar Netherlands.

Tuni 'yan sanda da masu kula da dabbobi a jirgi mai saukar Ungulu suka bazama neman su a ciki da wajen kauyen Oldeberkoop da ke arewacin kasar.

An bukaci mazauna kauyen da su kulle kofofi da tagogin su tare da zauna a cikin gida.

Kauyen Oldeberkoop wuri ne da ake ajiye nau'i daban-daban na Maguna a wurin ajiye dabbobi da ke Felida, su na kuma kokarin sama musu matsuguni na din-din-din a kasar Afurka ta Kudu.