Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Inganta harkokin kudi ta fasahar zamani

A ranar Juma'a ne ake kammala taron tattalin arziki na duniya a kan nahiyar Afrika, a Kigali babban birnin Rwanda.

Mahalarta sun yi ta tattaunawa kan yadda za a kyautata harkokin kudi ta amfani da fasahar zamani.

Hakan ta sa muka gayyaci Dr Nazifi Darma, wani masani a kan tattalin arziki domin ya dan yi bayanin yadda harkokin kudi ta intanet suke tafiya.