Ba za mu je yajin aiki ba— 'yan kasuwar Abuja

Image caption 'Ya'yan kungiyar Kwadigo ta NLC

A Najeriya, a yayin da kungiyoyin kwadago na NLC da TUC ke shirin shiga yajin aiki a kasar saboda karin kudin mai, kungiyar 'yan kasuwa da masana'antu reshen Abuja ta bukace su da su dakatar da wannan yunkuri na su.

A cikin wata sanarwa, shugaban kungiyar 'yan kasuwan ta Abuja, Mista Tony Ejinkeonye ya ce yajin aikin da kungiyoyin kwadigon su ka kira bai kamata ba, saboda bai kamata tattalin arzikin kasar ya kara shiga cikin tarnaki ba.

Kungiyar 'yan kasuwan ta Abuja ta bukaci kungiyoyin NLC da sauran 'yan Najeriya da su marawa gwamnatin tarayya baya a wannan lokaci, tana mai cewa tun a shekarun baya ta sha bayyana cewa ci gaba da biyan kudin tallafin mai ba abu ne mai yiwuwa ba.

A ranar Asabar ne kungiyoyin NLC da TUC suka bai wa gwamnatin kasar wa'adin kwanaki 4 da ta janye karin kudin man fetur da ta yi ko su tafi yajin aiki.

Kungiyoyin suka ce talakawan Najeriya na cikin mawuyacin hali, dan haka bai kamata a kara musu wata wahalar da karin farashin man fetur ba daga Naira 87 zuwa 145.

Suke ce "mun bada wa'adin ranar Talata 17 ga wannan watan, matukar abu wani mataki da gwamnati ta dauka, za mu bazama yajin aiki na sai baba ta gani da ya hada da ma'aikatan gwamnati, da na bankuna, da gidajen saida mai da sauran su.

Kungiyoyin dai sun bukaci al'ummar Najeriya da su gaggauta sayen abincin da zai wadacesu saboda yajin aikin da za a tafi, dan ko kasuwanni ma ba za su bude ba a lokacin.