Canada ta samar da manhajar hangen nesa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption sama mutum 800,000 suka tsere daga gidajensu

Gwamnatin kasar Canada ta samar da wata manyar wayar da za ta baiwa mutanen garin McMurray da aka kwashe daga lardin Alberta damar ganin hotunan giudajensu ta tauraron dan'adam.

Sai dai Ministan harkokin cikin gida na lardin Alberta, Danielle Larivee ta yi gargadin cewa hotunan ka iya tayar da hankali.

Ta kara da cewa manufar samar da manhajar ita ce ba wa jama'a damar samun bayanai na gaskiya.

Sama da mutum 800,000 wutar daji ta tilasta wa barin gidajensu a garin McMurray a cikin mako biyu.