An dakatar da wasan Man U na karshe

Filin wasa na Oldtraford
Image caption Jami'in 'dan sanda tare da kare da ke bincike

An dakatar da wasan karshe da kungiyar kwallon kafa ta Manchester United za ta kara da Bournemouth a kakar wasan bana saboda wani kunshi da aka gano a filin wasan .

An kwashe mutanen da ke zaune a bangaren Stretford da kuma bangaren Sir Alex Ferguson kafin a dakatar da wasan kuma an shigo da karnuka cikin filin domin su binciki wuraren da 'yan kallo suke zama.

Sai da aka jinkirta lokacin da kungiyoyin biyu za su fafata da juna, kuma daga bisani 'yan sanda suka bayar da shawarar dakatar da wasan.

Jamian tsaro sun dinga sa ido a kan 'yan kallo lokacin da suke barin filin.

Manchester ta ce 'Saboda kunshin da aka gani a wani bangare na filin wasa, an dakatar da wasan yau bisa shawarar da 'yan sanda suka bayar'.