An lalata kunshin wani abu a Old Trafford

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sojoji na janye motar da ta lalata kunshin

Jami'an soji masu kwance bom, sun lalata kunshin wani abu da aka ajiye a filin wasa na kulob din Manchester United, Old Trafford.

An tura sojoji filin wasan ne domin su gudanar da bincike kan kunshin da aka gani wanda ba a yarda da shi ba.

Kunshin abin da aka gani ya sa an dakatar da wasan kulob din na karshe a gasar Premier ta England, 'yan mintoci kafin a fara shi.

Dubban 'yan kallo ne aka fitar da su daga cikin filin wasan kafin a fara fafatawar tsakanin Mannchester United da Bournemouth.

Jami'an gasar ta Premier na kokarin tsayar da sabon lokaci na buga wasan.

Idan kulob din na Manchester na son shiga gasar zakarun turai na badi, sai ta zuwa kwallaye 19 a ragar Bournemouth, batare da ab ci ta ba.