Za a murkushe Polio a Pakistan

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Za a kawo karshen Polio a Pakistan

Hukumar lafiya ta duniya ta ce nan da wasu 'yan watanni za a murkushe cutar shan-inna ko polio a kasar Pakistan.

Wakilin Hukumar a kasar, Dr Michel Thieren ya shaida wa BBC cewa rahoton da suka samu na adadin wadanda suka harbu da cutar a wannan shekarar a kasar Pakistan da Afghanistan bai taka-kara-sun-karya ba.

Ya dai bayyana hakan ne lokacin da aka kaddamar da wata gagarumar shelar yaki da cutar a kasashen biyu, inda suke sa ran yin riga-kafin cutar ga yara miliyan tara a cikin shekaru uku masu zuwa.

Masu tayar da kayar-baya dai sun sha yin cikas ga kokarin yaki da cutar a kasashen, sakamakon adawar da suke yi da allurar.