'Yan gudun hijira na cikin garari — Angelina Jolie

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mr Grandi ya ce ya kamata a fito da tsari na hakika don tsugunar da masu gudun-hijira.

Wakiliyar majalisar dinkin duniya ta musamman kan 'yan gudun hijira, Angelina Jolie-Pitt, ta yi gargadin cewa shirin bai wa 'yan hijirar tallafi ya fada cikin garari.

Ms Jolie-Pitt ta shaida wa shirin BBC na World on the Move cewa "yawan rikice-rikice da kuma mutanen da hakan ke rabawa da gidajensu ya yi matukar karuwa" kuma shirin tallafa musu ba ya aiki.

Tun da farko dai, Babban jami'in Hukumar da ke kula da masu gudun-hijira ta majalisar dinkin duniya, Filippo Grandi ya nanata bukatar da ke akwai ta kasashen duniya su yunkura wajen magance matsalar masu gudun-hijira a duniya.

Ya shaida wa BBC cewa akwai bukatar hannu da yawa wajen daukar dawainiyar dubban 'yan gudun-hijira a duniya maimakon kasashe kalilan da ke taimakawa wajen tsugunar da su.

'Yara na shan wahala'

Mr Grandi ya ce ya kamata a fito da tsari na hakika don tsugunar da masu gudun-hijirar, yana cewa kasa da kashi daya bisa dari ne na miliyoyin 'yan gudun-hijirar da suka bazama duniya aka sake tsugunar da su a wata kasa.

Ita ma kungiyar kare hakkin yara ta Save the Children ta koka da yadda yaran masu gudun hijira ke fama da rashin makarantu.

Kungiyar ta ce yaro guda ne daga cikin yaran masu gudun-hijira hudu ke shiga makarantar sakandare.

Kungiyar ta yi gargadin cewa rashin fadada karatun yaran zai iya jefa su cikin talauci, kuma hadari ne sosai ga tsaro.

Wannna dalili ya sa kungiyar ta yi kira ga gwamnatocin kasashe da ma hukumomin agaji da su samar da wani tsari da zai tabbatar da cewa ba bu wani yaro dan gudun hijra da zai kasance a zaune ba tare da yana zuwa makaranta ba