An samu sabani tsakanin Senegal da Gambia

Hakkin mallakar hoto

Shugaban kasar Gambiya, Yahya Jammeh ya ce ba zai daga kafa ko kadan ba a takaddamar da kasarsa ke yi da Senegal, duk da cewa ministocin harkokin wajen kasashen biyu suna ganawa don shawo kan matsalar rufe iyakar kasashen.

Mista Jammeh ya ce ba ya wani tunani na sasantawa da Senegal, saboda a cewarsa Senegal din ce ta rufe iyakarta da Gambiyan.

Masu motocin dakon kaya a kasar Senegal ne suka fara rufe iyakar lokacin da Gambiyan ta ninka musu harajin da suke biya na shiga kasar da motocinsu.

Rufe iyakar dai ta janyo karancin kayayyakin masarufi a kasashen biyu.