Za a hukunta kamfani ko ma'aikatar da ta dakatar da aiki a Venezuela

Hakkin mallakar hoto Getty

Yayin da kasarsa ke fuskantar matsalar tabarbarewa tattalin arziki, shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro ya yi barazanar kama duk wani kamfani ko masana'antar da ta dakatar da aiki.

A wani jawabin da ya yi ga magoya bayansa, Nicolas Maduro ya zargi masu masana'antu da yi wa gwamnatinsa zagon-kasa, don haka a cewarsa ya kamata a garkame su a gidan yari.

'yan kasuwa da dama a kasar na fama da karancin kudaden waje da za su yi amfani da su wajen sayen kayan sarrafawa a masana'antunsu.

A bangare guda kuma, 'yan adawa na zanga-zanga da nufin yin kiranye ga shugaba Maduro domin a sauke shi daga mukaminsa.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaban kasar ya kafa dokar-ta-baci domin dakile abin da ya bayyana da mamayar kasashen waje, wadanda yake dora wa alhakin tabarbarewa tattalin arzikin kasarsa.