Za a bai wa Libya makamai saboda IS

Za a bawa Libya Makamai domin yakar IS
Bayanan hoto,

Za a bawa Libya Makamai domin yakar IS

Kasashe 25 cikin har da Amurka sun amince su ba wa gwamnatin hadin kai ta Libya da ke da goyan bayan MDD makamai, domin hana kungiyar IS kwace karin wata kasa a arewacin Afurka.

Kasashen sun ce za su sassauta takunkumin makaman da aka sawa Libya domin samawa dakarun sabuwar gwamnatin dake Tripoli makamai.

Praministan Libya, Fayez al-Sarraj, ya ce kungiyar IS wata babbar barazana ce kuma samun taimakon kasashen waje na da muhimmanci idan har ana san samun nasara a yaki da ta'addanci.

Fayez al-Sarraj, ya ce muna da babban kalu bale a gaban mu wato ta'addanci da yakar IS.

A saboda haka mun kafa dakin aiki na musamman, kuma muna fatan za'a hada kai a yakin.