Sojojin Nigeria sun kama masu fasa bututun mai

nigeria amry

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Sojojin Najeriya sun sha alwashin ladabtar da masu fasa bututan mai.

Rundunar sojin Najeriya ta ce kama wasu daga cikin 'yan kungiyar tsageru ta Niger Delta Avengers wadanda ake zargi da fasa bututan man fetur a yankin Naija Delta.

Kakakin rundunar sojin kasar Kanar Rabe Abubakar ne ya tabbatar wa BBC wannan labari.

Sai dai bai yi karin bayani kan yawan mutanen da aka kama ba.

Amma wasu rahotanni na cewa a cikin wadanda aka kama har da wani shugaban kungiyar.

Kungiyar dai ta dauki alhakin hare-haren da aka kai kan wasu bututan kamfanin mai na Chevron, tana mai cewa ta dauki matakin ne saboda "rashin adalcin" da ta ce ana yi wa mazauna yankin.

Fasa bututan man dai ya jefa kasar cikin duhu, ganin cewa su ne ke samar da gas din da ake amfani da shi wajen samar da hasken wutar lantarki.