Sulhunta makiyaya da manoma a Nigeria

Image caption Ana zargin Fulani da kai wa manoma hare-hare.

Shugabannin kungiyoyin Fulani da na makiyaya a Najeriya sun yi wata ganawa a Abuja don tattaunawa a kan zargin da ake yi wa Fulani makiyaya na kai hare-hare a kan wasu al'ummomi a kasar.

Manufar taron, wanda aka yi a karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa'ad Abubakar, ita ce zakulo hanyoyin da ya kamata a bi don hana aukuwar rikice-rikicen da ake samu tsakanin makiyaya da manoma, da ma wasu matsalolin da ake zargin Fulani da haifarwa.

A yayin taron an kafa kwamitoci bakwai, kuma a kowanne kwamiti akwai kwararru fannoni daban-daban domin suyi nazari su zakulo shawarwarin da suka kamata domin hana aukuwar irin wadannan matsaloli.

An kuma bawa kwamitocin mako biyu su kammala aikin da aka dora musu.

A wajen taron an tattauna yadda za a bullo da sababbin hanyoyin da za a bi wajen tsugunnar da fulani da kuma kawo karshen wannan rikici na fulani makiyaya.