Za a rage wa 'yan Nigeria miliyan 8 raɗaɗin talauci

Image caption Ana fama da matsanancin talauci a Nigeria

Gwamnatin Nigeria ta ce fiye da 'yan ƙasar miliyan takwas ne za su amfana daga rabin Naira tiriliyan daya na shirin rage raɗaɗin talauci a shekarar 2016.

Za a ciyar da yara miliyan 5.5 a makarantu 200 a kashin farko na shirin ciyar da yara 'yan makaranta.

Kazalika, shirin zai bai wa fiye da ƙananan 'yan kasuwa miliyan 1.6 damar samun bashi.

Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin babban mataimakin shugaban ƙasa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Mista Laolu Akande, yayin da yake ganawa da manema labarai.

Ya ƙara da cewa mutane miliyan ɗaya da ke cikin ƙangin talauci za su samu naira dubu 60 a cikin shekara, inda za a dinga ba su naira dubu biyar kowanne wata.