An yi dashen azzakari na farko a Amurka

Hakkin mallakar hoto Stellenbosch University
Image caption Likitocin da suka yi wa Thomas Manning aiki.

Likitoci a Amurka sun ce wani asibiti a Boston a ƙasar, ya zamo na farko da ya fara yin dashen azzakari kuma aka samu nasara.

Thomas Manning, mai shekara 64, ya samu sadakar mazakuta, shekaru uku bayan yanke masa azzakari da aka yi sakamakon cutar daji.

Manning ne mutum na uku a faɗin duniya da aka taɓa yi wa irin wannan dashen.

Ana sa ran cewa nan da 'yan watanni masu zuwa, Thomas zai fara yin fitsari da kuma saduwar aure da sabon azzakarin nasa.

Likitoci fiye 50 ne dai suka sanya hannu a lokacin aikin dashen wanda ya ɗauki awa 15.