Nigeria: An yi hatsaniya a majalisar wakilai

Image caption 'Yan majalisar jam'iyyar APC sun nuna goyon bayan janye tallafin yayin da na PDP ke adawa da hakan

A ranar Litinin ce aka yi wata hatsaniya a majalisar wakilan Najeriya tsakanin 'yan jam'iyyar APC mai rinjaye da ta PDP, mai adawa.

Al'amarin ya faru ne bayan da shugaban masu rinjaye na zauren, Femi Gbajabiamila, ya nemi 'yan majalisar su amince da ministan mai na ƙasar, Ibe Kachikwu, ya shigo zauren domin yin bayani kan ƙarin kuɗin mai.

'Yan jam'iyyar PDP ne dai suka nemi hana ministan ya shigo, da manufar yin ramuwar gayya kan ƙin amincewa da 'yan majalisa na jam'iyyar ANC suka yi kan ƙoƙarin cire tallafin mai da gwamnatin PDP ƙarƙashin jagorancin Goodluck Jonathan ta yi, a baya.

Sai dai kuma daga baya an amince ministan ya shiga zauren domin yin bayani, bayan wani zaman sirri da majalisar ta yi.

Majalisar dai ta gayyaci Ibe Kachiku ne domin ya yi mata karin bayani dangane da matakin da gwamnatin Najeriyar ta dauka na janye tallafin man fetur da kuma karin kudin man daga Naira 86 da kwabo 50 zuwa Naira 145 a makon da ya gabata, matakin da ya janyo ce-ce ku-ce a cikin kasar da kuma barazanar tafiya yajin aiki daga Kungiyar Kwadago NLC.

Sai dai har zuwa lokacin da majalisar ta kawo ƙarshen zamanta na ranar Litinin ɗin bata yanke hukuncin da za ta ɗauka kan wannan lamari ba.

Ibrahim Mijinyawa ya zanta da Honorable Magaji Da'u Aliyu wani dan majalisar wakilan tarayyar, kan wannan zama nasu, ga kuma yadda hirar ta kasance:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A makon da ya gabata ne dai gwamnatin Najeriya ta sanar da ƙarin farashin man fetur, al'amarin da ya jawo kace-nace.