'Yan achaɓar Saliyo sun ƙaurace wa tituna

Hakkin mallakar hoto Getty

A ranar Litinin ne 'yan achaɓa damasu motocin haya suka ƙaurace wa tituna a Freetown, babban birnin Saliyo.

Hakan ya faru ne sakamakon dirar mikiyar da jami'an tsaro suka yi musu domin tirsasa su bin dokokin hanya.

'Yan achaɓar sun ce sun janye daga titunan ne sakamakon tsangwamar da suke fuskanta daga 'yan sanda.

Wannan al'amari ya jawo matsananciyar takura ga al'ummar birnin Freetown sakamakon rashin abin hawa.