Ba na ƙyamar Musulmai —Trump

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mista Trump ya bukaci Musulmai su bai wa 'yan sanda hadin kai.

Mutumin da ake sa ran zai yi wa Republican takarar shugabancin Amurka, Donald Trump, ya ce ba ya ƙyamar Musulmai amma yana ƙyamar masu tsattsauran ra'ayi.

A wata hira da ya yi da gidan talabijin ITV da ke Biritaniya, Mista Trump ya yi kira ga Musulmai da su rika yin aiki tare da 'yan sanda ta yadda za su sauya wa masu tsattsauran ra'ayi halayensu.

Ya mayar da martani ga kalaman da Firai Ministan Biritaniya David Cameron ya yi a kansa, inda ya ce shi [Trump] a matsayin "wawa, mai son raba kan mutane" saboda ya ce zai hana Musulmai shiga Amurka idan ya ci zabe.

Da aka tambaye shi, ko ya sauya ra'ayinsa ne, sai ya ce "dama duk abin da na fada na yi ne a matsayin shawara".