Dalilin sanya dokar ta baci a Venezuela

Hakkin mallakar hoto Getty

Gwamnatin Venezuela ta wallafa cikakken bayani a kan dokar ta-bacin da shugaban kasar Nicolas Maduro ya kafa sakamakon fadawar kasar cikin rikicin siyasa da na tattalin arziki.

Dokar za ta ci wa'adin kwana sittin, kodayake za a iya sake tsawaita ta da kwana sittin.

Za a baiwa sojoji da wasu kwamitoci da aka kafa damar rarraba kayan abinci.

Dokar ta baiwa mahukunta damar rage tsawon ranakun aikin kamfanoni da sauran 'yan kasuwa don rage bukatar wutar lantarki.

Shugaba Maduro ya ce daukar matakin ya zama wajibi saboda a yaki masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon-kasa.

A halin da ake ciki dai 'yan adawa sun dukufa wajen ganin an sauke shugaban kasar daga mukaminsa ta hanyar yi masa kiranye.