Direbobi na yajin aiki a Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana yajin aiki a Faransa

Direbobin manyan motocin daukar kaya sun rufe manyan hanyoyi a Faransa, sakamakon yajin aikin da masu adawa da sauye-sauye ga dokokin aiki a kasar, suka fara.

An samu cunkoson ababen hawa a manyan biranen kasar sakamakon zanga-zanga.

Ana sa ran nan gaba, ma'aikatan jiragen kasa su ma za su bi sahunsu, abin da zai jawo wa matafiya da maraice babban cikas.

Shugabannin kwadago sun ce suna san gaba daya hanyoyin sufurin Faransa su tsaka cak.

Shugaba Francoise Hollande kuma ya lashi takobin ci gaba da yin sauye sauyan, yana barazanar daukar mummunan mataki akan masu zanga idan har suka yi hatsaniya da 'yan sanda.