Jinkiri a zirga-zirgar jiragen sama a Nigeria

Image caption Ana yawan fama d karancin man fetur a Najeriya

Harkokin zirga-zirgar jiragen sama na Najeriya na fuskantar jinkiri sakamakon karancin man da jiragen ke amfani da shi.

Yanzu haka a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas a kasar, fasinjoji da dama da ke shirin yin bulaguro zuwa wasu jihohin kasar dama na kasashen waje, na can cirko-cirko.

Bincike ya nuna cewa da yawa daga jiragen da ke jigilar mutane sun dakatar da harkokinsu sakamakon karancin man jirgin sama.

Ga rahoton da wakilinmu Umar Sheheu Elleman ya aiko mana daga Legas:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti