Kotun Nigeria ta hana NLC yajin aiki

Kungiyar kwadago ta NLC tana shirin fara yajin aiki ranar Laraba
Kotun sasanta 'yan kwadago a Najeriya ta dakatar da kungiyar kwadagon kasar daga tafiya yajin aikin da take shirin farawa ranar Laraba.
Ministan shari'a na kasar, Barista Abubakar Malami wanda ya tabbatarwa BBC hakan, ya ce kotun ta yi hakan ne domin hana fadawar kasar cikin halin ni-'ya-su.
Sai dai kuma ministan ya ce dakatarwar ta wucin-gadi ce kuma gwamnati na ci gaba da tattaunawa da kungiyar ta kwadago.
Kungiyar kwadagon dai ta ba wa gwamnatin Najeriya zuwa karfe 12 na daren Talata da ta janye karin farashin mai da ta yi daga N86 zuwa N145, ko kuma ta tafi yajin-aikin sai illa-Ma Sha-Allahu.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, Minti Daya da BBC Safe 15/01/2021, Tsawon lokaci 1,07
Minti Ɗaya da BBC na Safiyar 15/01/2021, wanda nabela Mukhtar Uba da Sani Aliyu su ka karanto.