Muna bincike kan 'yar Chibok — Sojoji

Image caption Har yanzu dai akwai sauran 'yan matan Chibok din a hannun kungiyar Boko Haram.

Rundunar sojin Najeriya ta fitar da sanarwar da ta yi karin bayani game da daya daga cikin 'yan matan sakandaren Chibok din da aka ceto, mai suna Amina Ali.

Rundunar ta bayyana cewa, tare da hadin gwiwar 'yan kato da gora, watau Civilian JTF da suka kafa shingaye a kauyen Baale da ke garin Damboa, an ceto Amina Ali dauke da jaririnta.

Kazalika kuma an kama wani mai suna Mohammed Hayatu, da ake zargin dan Boko Haram ne, wanda ya ce shi ne mijinta.

Sojojin dai sun tasa keyarsu zuwa hedikwatar rundunar da ke Damboa, domin gudanar da bincike.

Bincike da aka soma tun farko dai ya tabbatar da cewa yarinyar na daya daga cikin 'yan matan makarantar Chibok din, wadanda Boko Haram suka yi garkuwa da su tun ranar 14 ga watan Afrilun shekarar 2014.

Sanarwar dai ta ce ba sunan yarinyar Falmata Mbalala ba, kamar yadda tun farko aka yi zato ba, kuma an kai ta da jaririn nata asibiti a cikin garin Maiduguri domin duba lafiyarsu.

Tunda farko dai wata mai fafutuka kuma farfesa a jami'ar Maiduguri, Hauwa Biu ce ta tabbatar wa BBC wannan labari.

Farfesa Biu ta ce an gano yarinyar ne sakamakon wata arangama tsakanin 'yan kato da gora da mayakan Boko Haram a kusa da dajin Sambisa.

'Yan kato da gorar sun samu nasarar fatattakar mayakan Boko Haram din, amma sun samu wata yarinya a tare da su da goyo a bayanta.

Daya daga cikin 'yan kato da gorar ne ya gane yarinyar a matsayin daya daga cikin 'yan mata makarantar sakandaren Chibok da aka sace a shekarar 2014.

Farfesa Biu ta ce, "Sai suka kwace yarinyar daga hannun mayakan suka kai ta garin Chibok kuma iyayenta sun gane ta.''

Mansur Liman ya tambayi Aboku Gaji, shugaban 'yan kungiyar sintiri ta Vilante a Chibok, wanda ya ga yarinyar, ko yaya suka gane cewar yarinyar itace?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti