'Nigeria ce kan gaba a tarun fuka'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Yadda ake amfani da na'ura wajen gano tarin fuka.

Masana kiwon lafiya sun ce Najeriya na sahun gaba cikin kasashen Afrika da aka fi samun masu kamuwa da cutar tarin fuka, a kowace shekara.

Hakan dai ya bayyana ne yayin wani babban taro na ƙasa kan tarin fuka na kwanaki biyu da aka kammala, ranar Laraba, a Abuja, babban birnin kasar.

Taron wanda ya samu halartar masana kiwon lafiya daga kasashen duniya da dama ya mayar da hankali kan irin matakan da ya kamata a dauka don rage yawan kamuwa da cutar a kasashen Afrika.

Daman dai hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ce ana tsammanin samun fiye da mutane miliyan hudu da za su kamu da cutar, a kasar, tsakanin 2015 zuwa 2020.