Nigeria: Kayayyakin masarufi na kara tsada

A Nigeria bisa ga dukkan alamu farashin kayan masarufi na kara hauhawa.

Cikin 'yan watannin nan farashin kayan bukatun yau da kullum na karuwa a duk fadin kasar.

Lamarin da yafi shafar kayan abinci, da sauran muhimman abubuwa.

Wannan na faruwa ne yayin da tattalin arzikin kasar yake kara samun koma baya saboda faduwar farashin mai.

'Yan Nigeria suna kokawa kan abinda wasu suka kira, matsanancin hali da suke fuskanta.