Otto: motar dakon kaya da ba ta da direba

Hakkin mallakar hoto Otto

Wani gungun tsofaffin ma'aikatan kanfanin Google da Apple da kuma Tesla, sun ƙera mota da ba ta da direba.

Motar mai sunan Otto, sun kerata ne domin maye gurbin motocin dakon kaya.

Da farko dai, motar za ta kasance ta dakon kaya kafi ta daukar jama'a.

Zuwa yanzu dai babu wasu bayanai game da lokacin da motar za ta soma hawa hanyoyi, ko kuma farashin ta.