Akwai barazanar yaduwar Zika

Hukumar Lafiya ta duniya ta yi gargadin cewa kwayar cutar Zika na iya bazuwa ga wasu sassan nahiyar Turai a wannan bazarar.

Kwayar cutar da sauro ke yadawa kan jawo haihuwar jariri da nakasar da ke shafar kwakwalwa, idan mace mai juna biyu ta kamu da cutar.

Hukumar lafiyar ta ce Yankin Madeira da Rasha da Georgia ne suka fi fuskantar hadarin samun cutar.

Sauran kasashen da ka iya samun cutar sun hada da Faransa da Sipaniya da Girka da kuma Italiya.

Har yanzu dai ba'a samu rigakafin cutar ba, wadda a yawancin mutane kan fara da mura.