'Yar Chibok ta gana da shugaba Buhari

Image caption Wata majiya ta shaida wa BBC cewa an duba lafiyar Amina Ali da jaririnta a asibiti.

Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da yarinyar nan 'yar makarantar Chibok, wadda aka ceto bayan ta yi fiye da shekara biyu a hannun kungiyar Boko Haram da suka sace ta.

An sami yarinyar, mai shekaru 19, tare da jaririyarta 'yar wata hudu a wani daji da ke kusa da kan iyakar Najeriya da Kamaru.

Yarinyar na daya daga cikin 'yan mata 219 da Boko Haram ta yi garkuwa da su daga makarantar kwana ta Chibok a watan Afrilun shekarar 2014.

Yarinyar dai daliba ce a makarantar Chibok din nan da aka ceto daga hannun Boko Haram, ta isa fadar shugaban Najeriya da ke Abuja tare da rakiyar gwamnan jihar Borno da wasu manyan jami'an gwamnati.

Wannan dai shi ne karon farko cikin shekara biyu da aka yi nasarar kuɓuto wata daga cikin 'yan matan Chibok fiye da ɗari biyu da 'yan Boko Haram suka sace.

Image caption An duba lafiyar Amina Ali da jaririnta.

Tun da farko dai rundunar sojan Nigeria ta ce ta miƙa yarinyar da jaririyarta ga gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima.

Ɗaya daga cikin dattawan yankin Chibok ya ce, yarinyar da aka ceto ta sanar da su cewa, dukkan sauran 'yan matan suna hannun 'yan Boko Haram a dajin Sambisa.

Rundunar sojin Najeriya ta ce tana tsare da wani mutum da suke zargin dan Boko Haram ne, da suka samu tare da ita, wanda ya ce shi ne mijinta.