Za a habaka rayuwar mata da 'yan mata a duniya

Gidauniyar Bill da Melinda Gates ta kudiri aniyar tattaro bayanai game da halin da mata da 'yan mata ke ciki a fadin duniya.

Gidauniya ta kebe kudi sama da dala miliyan 80 don inganta tattaro bayanan da kuma habaka ci gaban mata da 'yan mata a duniya.

Shugabar hadin-gwiwa ta gidauniyar Melinda Gates ce ta bayyana haka a wajen wani taro na duniya da aka yi wa lakabi da Women Deliver a Copenhagen, babban birnin kasar Denmark.

A cewar Halima Nuraddeen jami'a a wata kungiyar ci gaban mata matasa da dalibai ta Afirka mai cibiya a Abuja wannan kuɗi zai iya kawo sauyi a rayuwar mata da 'yan mata musamman a Najeriya da ma Afirka baki daya.