Gwamnoni sun goyi bayan Buhari kan farashin fetur

Gwamnonin Najeriya sun ce sun goyi bayan shugaban kasar Muhammadu Buhari a kan kara farashin man da gwamnatinsa ta yi.

Gwamnonin sun ce tallafin da aka sanya a kan man na fetur ba ya mafanar 'yan kasar don haka gara da aka cire shi.

A hirar da ya yi da wakilinmu, Yusuf Tijjani, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce za su dauki matakin rage radadin da karin farashin man zai yi ga 'yan kasar:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti